Saturday, 10 October 2015

Amaechi Ya Ziyarci Saraki, Ya Nema A Saukaka Mashi Bincike

Tsohon Gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi ya ziyarci Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki inda ya nema a saukaka mashi wajen tantancewa.
Tsohon Gwamnan Jihar Rivers Rotimi Amaechi
Amaechi yaje wajen Saraki be domin ya samu sauki a lokacin da za’a tantance shi a gaban majalisar.
Zaben Amaechi da akayi yana samun kalubalen sosai a majalisa domin sanatocin da suka fito daga Jihar shi har sun kai koke suna zargin shi da rashawa.
Gwamnatin Jihar ta fidda sanarwa inda ta bayyana cewa koda Amaechi ya zama minista, wanna ba zaya fidda shi daga bincike ba. Wata majalisa ta bayyana cewa Amaechi ya ziyarci Saraki a ranar Talata 6, ga watan Oktoba da misalin karfe 11:45 na dare, bai fita ba sai karfe 1.
Amaechi ya tafi ne tare da wani maitaimaka mashi inda ya bukaci Saraki daya manta baya sannan ya taimaka Mashi domin ya taallake.

No comments:

Post a Comment

publisher,advertisement,fun,cool,interesting,news,travelling,football